(Final) HUBBUL YAQEEN SERIES FIVE

Shi kuwa Sulaiman tunda ya wuce bai tsaya ko inaba sai a bakin gate din office dinsu, kaf ya tsaya tsam kamar wanda yaga wani dodo, sani ya manta oganshi yayi tafiya, ya tafi wajen wani comfrence da za’ayi a sokoto kuma zasuyi kamar kwana shida zuwa biyar basu dawo ba, to meyasa ma wai bai tuna ba sai a yanzu, wani tsaki yayi mai hade da takaici, said a yayi kamar minti biyar a bakin gate din office din nasu sanna ya tada mashin dinshi ya nufi gidan Alhaji day a basu haya domin ayita takare idan yanada wani gida ya canza musu ko kuwa asan yanda za’ayi kafin nan da zuwan kwanaki shida da oganshi zai dawo ya nemi transfer ya bar gari tun a kan layin gidan Alhajin ya fara ganin dandazon mutane ba adadi har ya iso kofar gidansa, me zai gani ga dukan alamu wani abu akayi ras! Gabansa ya fadi a wurinda shimfida take ya dire takalma yayi sallama ya mike hannu tabbas gaisuwar rasuwa ake yayi gaisawa aka ansa masa ya nemi ya gana da babban dansa, kasan cewar yasan sulaiman domin tare dashi akayi process din gidansu Sulaiman. Bayan da Sulaiman ya kara yi masa gaisuwa ya tambayeshi yanda haka ta faru, ya shaida mai matukar rudarwa, a jiya da dare ne yana bacci sai kawai akaga ya mike tsaye ya sauka daga kan gado, ya farayin da baya-dabaya yana ta ko’ina har ya fadi kasa, likitoci sun auna sun fada cewa sakamakon ganin wani mummunan tashin hankali da idon dan adam da kuma kwakwakwar sa basa iya dauka da yayi shiya hifar masa da wani matsanancin bugun zuciya da har yayi sanadiyar rasa rayuwarsa a nan take dirshan ya fadi a kasa hawaye suka riqa zuba a idanuwansa, al’amarinda yayi matukar bawa mutanenda ke wurin mamaki kenan hade da tausayin musamman babban dan Alhaji, lallashin shi aka dingayi har ya dawo cikin hankalishi ya daina kukan da yake. Shi kadai yasan abinda yakewa kuka tabbas shakkah babu akwai wani mummunan abu dake shirin faruwa dasu, gashi sub a yan gari ba yaya zai yi. Ya zabura ya mike ya sake gaisuwa yayi sallama ya wuce, dole subar garinan gobe-gobe ba domin sko yanzu lokaci ya kure musu bad a sun bar garin a yau, kara gudu yayi kamar wanda zai tashi sama domin kar dai wani abu yazo ya sameta domin kuwa Bilkisu shi c eta fado mishi a rai, kar dai wani abu yazo ya sameta.


Krar shit ta dawo masa da hankalin shi daga tunaninda yakeyi bai yi ni yar ya dauka ba kuma dai yaji bari ya dauka aljihu ya zara wayar shi sanan abakinshi Nuhu ya gani da sauri ya dayka ya karakan kunnensa, slamu alaikum ya fadawa alaikussalam, Sulaiman don Allah kayi hakuri kaga ban samu dammar kawo su uUmmi ba Wallahi jiya da sakiyar dare mamansu ta kuma da matsanancin ciwon ciki amai da gudawa tun sa’annan muna asibiti sai yanzu muka dawo, yanzu dai Alhamdulillahi ta samu sauki sosai, kayi hakuri fatun sannan ban masan ida wayana yake ba sai yanzu da muka dawo bare na kiraka na gagayama bazan samu dammar kawo su ummi ba kasan ya yanda al’amuran suke wallahi tun sannan bansamu nutsuwa ba sai fa yanzu da kaga na kiraka. Rasa ta cewa yayi can ya lalibo kalamai yace ai badamuwa Nuhu Allah dai ya bata lafiya ya tashi kafadarta sai munzo dubata nida Uwargidata tau amen, amee, Sulaiman, When sai kunzo, sai an jima ya katse wayar. Wani matsanancin gudu yakeyi kamar ranshi zai fiita ya nufaci gidanshi haiqan dearest!dearest! dearest! Yake fadi kamar wani mahaukaci, da karfi yasha kwanar gidansi, kicibis! Yayi da wani abin ban mamaki, Bilkisu ya hango tana fama dariya tana bye-bye da hannunta, kyar ya iso a gabanta, murmushi tayi ta nufaci inda yake sannu da zuwa ga baki daya ta jagula masa lissafi zauwa ke dawa kike bye-bye haka? Malam mu shiga daga ciki ai ko, biye kawai yake da ita, suka shiga cikin gida su waye suka zo wurinki ne haka, ni fah da farko duk kin tsoratani n zata ko ke kadaice a gidan duk hankalina ya tashi, wani kallo tayi mai alamar ina ma fushi da kai, eh ai dole kace haka ai, ta wani shagwabe murya sanna tace stunda kasan Nuhu ya kawo su Ummi! Shine ka tafi abinka ka shallake, to sune nakewa bye-bye da yazo daukan su, nayi-nayi ya jiraka amma yaki ta, su ummi!! Kuma Nuhun ne yazo daukan su!! Mikewa yayi inna lillahi wa inna illaihi raji’un, a firgice itama ta mike hakika sulaiman dinta ba karamar razana yayi ba to muje na razana a cikin abinda ta fada. Lafiya dearest meya faru meye don Allah gayamin, Bilkisu tashi ki had kayanki gobe-gobe zamubar garinnan, me ya faru ka gayamin! Ta daka masa tsawa tana mai zubarda kwallah batareda tasan ma tayi ba, da kyar ya kwantarda hankalinshi ya zaunarda ita kana ya bayyana mata duk abinda ya faru tun daga farko har rasuwar Alhaji da rashi lafiyar mata Nuhu duka ya bayyana mata shiru tayi ta kasa koda motsa dan yatsan ta akan tsananin firgitarda tayi Bilkisu! Bilkisu! Ga baki daya batajin abinda yake fada, said a ya wujijigata da karfi sanna ta dawo ayyacinta, Bilkisu karki damu gobe-gobe zamu bar garinan a’a ba sai na ta fada tana mai fashewa da matsanancin kuka, a’a Bilkisu ki bari gobe tunda sassafe, a’a ta durkusa kasa ta rike masa guwayyunsa na rokka don Allah Mubargarin nan a yau din nan, nunfashi ya aje, to shikenan jeki hado kayanki mu wuce, karki damu sa sauran kayan, idan nazo karbar transfer letter din azan wuce dasaura, shiga tayi ta tattara kayanta shima tattara nashi kayan yakeyi, sai a yanzu ta gane lallai wayannan basu Ummmi bane, bayan da ta zuba maganin sai taga duk sun wani kamar rikice, ta tuna sanda ta aika amina kitechen ta dauko mata plate sam takasa shiga a kitchen din, sa yanzu ta fahimci tun lokacinda ta zuba maganin basu sake takawa daga cikin falon ba. Tsam ta mike tunawa tayi da yanda Ummi ta dauko jug a cikin feeg wanda ta cika da drinks din kwakwa ta wankada akan kofar fita falon wanda zata fitar da mutum zuwa ta gane da gangan ta fadi ta zubar da drinks din don dai kawai su samu su fita. Kamala hada kayan tayi a dai-dai lokacinda shima y agama kamala nashi muje ko yace ta janyo hijabinta data ajiye kalar kayanda ta saka tace eh, muje tare suka nufi hanyar fita, tsayawa sulaiman yayi ya kalli gidan da kyau ya gayda kai ya wuce suka kulle gida sun juya zasu wuce sukaji an kyalkayale da wata mahaukaciyar dariya, duban juna kawai sukayi ba tareda sun ce ko kalaba sukaja akwatunansu sai a kan titi suka tsaya, wani mai a daidaita suka tsayar, garge zaka kaimu, yasa kayansu ya nufaci garge din, misalign karfe uku da rabi ne narana garin ana tsananin zafi, wurin fifa ya tsayar day an layin su, jira suke ya dauko musu hannu su wuce,


ji tayi kamar ana girgiza kasa, ruguzum komi na wurin ya fara rusgawa cikin kasa, kuwwa da hrgowar jama’a kawai kakeji, motuna da baburra sairuguzawa sukeyi kamar an cilla a dai daita sahu su, sulaiman ya runtuma cikin, caf tasa hannuwanta ta cafkoshi, wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta shiga kuka take tana hargowa karka tafi ka barni tana rike da hannunshi sauran jikinshi kuwa yana lib, hannunshi ya fara subuce mata tana mai tsala uwar kuwa tsundum ya fada yana kiiran sunanta Bilkisu! Bilkisu! Sulaiman ya ingi zata, caraf ta dawo daga wanna mummunan mafarki zatace ko tunani, ita dai tasan a zahiri taga wannan abu ya faru, lafiya me kike tunani haka? Sulaiman ya katseta, waige-waige take da idanuwata cikin mawuyacin hali, ke meye? Meya faru? Jin ta kama hannuwanshi ta jinike da nata, a jiyar zuciya yayi, karki damu masoyiyata insha Allahu zamu isa gida lafiya, gobe irin wannan lokacin kina gaban Umma, ya fada yana zolayata, duk day a kokarin da tayi wajen gani tayi murmushi ta kishingida dai-dai wajen ‘yanBauchi aka ajiye su, sune passengers na farko da suka fara loda a motar, bayan an saka masu kaya a mota, suka shiga ciki mota suka zauna suna jiran zuwan sauran passengers, zaunawar su keda wuya dum! Sukaji ko ina yayi rufe da wani matsanancin duhu smai tsananin muryoyi sukaji kala-kala ta yadda ba zasu iya tantance ko murya mace, namiji? Ko kuwa karamin yaro ba.


Gargadinsu a kayi da murya mai kaushi akan suyi gaggawar fita daga cikin motar na su koma ya zuwa gidansu da suka baro, muddin kuwa sukace zasuyi taurin kai, kuwa zasu hadu da matsanancin hadarin motar da zatayi sanadin halkar duk wani passenger da ke a cikin motar, sanna kuma aka wayanda basuji basu gani ba, domin kuwa driver matarshi ta haihu kwana biyu yayi saura ayi biki, idan sukayi sanadiyar mutuwar wazai dauki nauyin iyalishi kuwa wanda yake kan gaba a kusa da driver dan makarantane shi kadai ne namiji a gidan su, mahaifinsa ya rasu mahaifiyarsa ke wahala wajen ganin ta biya masa kudin makaranta. Ita kuwa wannan matar ‘yaranta duka biyu marayu ne ‘yan uwan mahaifinsu sun kwace musu dukiyarsu, wajen ‘yan uwanta zataje neman agaji. A haka akaci gaba da lissafo musu ko wane passenger da abinda yake kunshe dashi duk domin dai so fita daga cikin motar bayanta aka gama gargadinsu, wayau! Sukaga ko’ina ya yaye, kuma motar da suke ciki hart a cika da passengers, kamar yadda aka shaida musu haka kuwa suka gani, duk wayanda aka lissafa musu a motar su da ne ke ciki. Kallon juna sukayi ba yareda sun samu dammar furta wata kalam ba, wayar direba ce yita wau kara, dauka yayi tareda sallama, slamu alaikum lafiya kalau wallahi, a’a alhamdulillahi mun gode Allah, amen, amen, sosa kunnenshi yayi yana ‘yar dariya, eh saura kwana biyu ma ayi bikin ai ina Allah ya yarda. Dam gabansu yafadi suka sake duban juna da karfi, tare suka hada baki dakata!! Duk motar kowa ya jiyo ya ba, ana saka kayane a but da hanzari suka bade murfin motar suka fito, mun fasa tafiya Sulaiman yace gaywa condester, don Allah kuyi hakuri wallahi mun fasa tafiyar me kace malam, kamar ya ya kunfasa lafiya wanna aima maganar banzace, duka mutanen wurin suka taso wasu na bayadda hakuri wasu na zugawa, anan dai aka samu wani dattijo mai hankali da sanin ya kamata, yace tunda ai ga wasu passengers nan ba sai kawai su shiga a madadin wayannan ba, ai wannan abun bai kai na wani dogon bayani ba, sukayi masa godiya suka nemi a dai-daita sahu suka sake saka kayansu suka nufi gidansu da suka saka baro, suka bar mutanen garage din kowa tana mamakin wayannan mutane haka, su kadai suka san dalilin da yasa suka bar motar, ba kuzari mai adai-daita ya sauke su a kofar gidansu, said a suka yi kamar minti bakwai a tsaye suna kallonn-kallo sanna Sulaiman ya bude gida suka dunguma a ciki, ga baki daya duniya tayi masu zafi komai ya kulle musu, sun ma rasa ta inda zasu fara bamai cewa kowa ko kala, suka isa bakin kofar falo ya saka key a ciki yana kokarin mirdawa ya bude kofar falon, kiririn,kirin wayar Sulaiman tayi kara su duka suka zabura da karfi, hannu yakai aljihu ya ciro wayar, sunan mahaifinshi ya gani ya bayyana a gaban screen din wayar shi, dauka yayi, yayi kokarin boye duk wata damuwar shi, da ke tattare dahshi, slamu alaikum Abba ina wuni lafiya kalau, lafiya kalau take, komai Alhamdulillahi, Na’am Abba na nameye ya tambaya yana mai nuna mutukar mamakinshi a filli kamar a gaban Abban nasa yake, kallonta yayi da hanzari eh yayi murmushin yake yace amen, har yanzu kallonta yake yi, to amen baba ehan, ya katse wayar har yanzu kallonta yakeyi, ga baki daya hankalin shi a tashe yake itama kallon nashi take yi, meye ta tambaya tana kallonshi wai Abbane yake tayani murya, wai a dazun nan Ummata ta kira ki a waya, kika gaya mata mun dawo ne daga Asibiti likita ya tabbatar mana da cewwa kinda juna biyu na tsawon wata biyu, dirshan ta fadi zaune barkewa tayi da wani matsanancin kuka, shima, sulaiman zama yayi a dai-dai kusa da ita sai dai wannan karon ba lallashinta yakeyi ba, hada tagumi yayi ta fada kogon tunani, shi ba abinya fada ta gida ba, a can hankalin su ya tashi, kuma ma zai iya yuwa idan wani yace zaizo a kasheshi a kan hanya sunfi minti goma anan zaune, sa’annan Sulaiman ya mike ya iyadda bude kofar falon su duka suka shiga ciki,


jawo akwati takeyi itama suka nufi daki ji tayi kamar an ja mata kafa jicce ta fadi kass ram! Yunkurawa tayi ta tashi amma ta kasa, wasu taurarin wahala ta ringa gani sunayi mata yawo, yarda tashi akwatin yayi ya nufo inda take da gudu, yanka kokarin tada ta, lumshe idanuwanta ta farayi, tun tana iya budsu har takai ga duka suka rufe rungumeta yayi ya kwala uwar ihu, da hanzari ya tallabeta da gudu ya fito baima tsaya ta wani rufe gida ba. Mijin Khadija yayi kicibis dashi ya dawo, da karfi ya tsayadda mota, Sulaiman da gudu ya shiga, Asibiti, asibiti! Da isarsu asibiti aka daurata saman keke da gudu aka wuce da ita emergency, gaf aka rufe kofar emergency aka dakatar dashi daga yunkurin shiga cikin dakin da yayi, jiginawa yayi a jikin bango emergency zaune yayi a nan wurin ya fara kuka ne ya ringa lallashi da kyar da sidin goshin daina hargowarda yake ya zama hawaye kawai ke zuba daga idanunsa, nurse c eta fito da fara’arta da kafri suka mike su duka sister ya lafiyar jikinta, zan iya shiga yanzu, don Allah ku bari na shiga nag anta, Sulaiman k eke jero wayannan zancen duk shankalinshi a tashe relax malam cogratutaltion ma, wani kallo yake mata me kikace? Cewa nayi congratulation matarka na dauke da JUNA BIYYU na tsawon wata biyo, kuma zaka iya shiga ka ganta, za ma kaiya tafiya da ita, because she is out of danger known. Bai jira ta kommala jawabinta ba yaruga da gudu zuwa cikin inda dearest dinshi take, zaune ya taradda ita tana kallon yan yatsunta tsaye ya tsaya cak, kamar tasan dashi ta daga kai suka hada ido, ya karaso inda take ya rungumeta yana zubarda kwalla, Alhamdulillahi kin tsoratani, don sAllah kada ki sake yimin irin haka. A nan aka sallame su daga asibiti maigidansu Khadija ya maidasu gida, sukayi masa godiya sun ma rasa zaune kawai sukayi kamar masu ansar gaisuwa, kiran mariba akayi, suka tashi sukayi alwala, ya jagoranceta sukayi sallah, mikewa yayi ya fada kichen a dafa mata indomies, a wani bangare na rayuwarshi harga Allah dadi yakeji mara misaltuwa, matarshi nada ciki, kenan zai zama baba, zubo indomie yayi a flate ya kawo masu a nan bedroom dinsu tareda rowan da zasu sha, aka kira isha’I suka mike suka sauke farali, suka jawo kwanon abinci sukaci sukasha ruwa, ta tashi da dauki kwanuka da ni yar ta kai kitchen karaf ya amshe, no wannan ba aikin ki bane yanzu, zauna ki huta, kada ki wahaltamin da baby, duk da irin halin da suke ciki said a tayi yar dariya, duk kunya ta lullubeta, ya dauki kwanuka yaje ya ajiye ya dawo, suka yi addu’a suka kwanta. Wayyo!! Wata kara aka buga mai mai matukar firgitarwa zunbur suka sauka daga kan gaso jan abu sukaji anayi a falo, kasan tys idan ana jan abu akanshi zai ringa bada wani sauti daban, kuka sukeji anayi matsananci, a hankali suka tattaka ya zuwa bakin kofar daki yaddazasu iya hango abinda ke faruwa a falon, da baya sukaja da kafri saka makon ganin wanan tashin hankali da basu taba gani shi ba, wata mace ce ko ince budurwa wace bata wuce shekara goma sha takwas zuwa sha tara ba, ake ja, batareda suna ganin mai jan nata bag a baki daya jikinta jinine faca-faca, kama kuwa kadan ya rage ya rabuda gangar jikinta, rokonsu take tana kuka don Allah ku taimaka mini, karaja sukeyi da baya suka rungume juna suka kankame waje daya, wuf tayi ta nufo su da niyar ta cafke su, kamar an wulla ta ta fada can gefe daya, sake mikewa tayi kanta yana shillo ta kara nufo su amma kamar a karon farko ma sake wurgata akayi, kuwa take kala-kala iri-iri tana yunkurin kamasu amma ta kasa, su kuwa suka buga suka kara ja da baya suncakankame juna, duk wani yunkuri, na shiga cikin dakin tayi amma ta kasa Sulaiman ne yayi karfin hali ya ja kofar daki ya rufa da karfi ya dawo daga baya. Duk hargowarda takeyi a kunnuwansu yake, addu’a suka yi suka tottafa ko’ina suka haye kan gado ko runtsawa ba wanda yayi-sai yanzu Bilkisu ta gano dalilin da yasa ta kasa shigawa acikin dakin, maganinda baban nan ya btane, haka suka zauna ba wanda ya koda runtsa idanuwashi,


sai a shiyoyin asuba su duka bacci ya sace sub a tareda sun sani ba Sulaiman ya fara falkawa, kasa rufe bakinsa yayi sakamakon kashin ganin matarshi da yayi akan gado, kofa ya gani bude, a hankali ya tashi ya fara tafiya yana duba kofar, can ya hango Bilkisushi a falo zauna murmushi, zo dearet, zo mu karanta Qur’ani kama meye yayi kadan ya cuta mana, shi nake karantawa kazoo mu sauke Qur’ani a yau dinna, ajiyar zuciya yayi ya sauke nunfashi da karfi okay bari na dauko nawa Qur’anin, a’a ai gashi na dauko duka zo kawai mu karanta, fitowa yayi ya nufa ci falon ya tsallaka ya fada cikin falon, sai dai kuwa abinda bai saniba Bilkisunshi tana kwance sa bias gado tana sharer bacci abinta. Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka itama kamar yadda Sulaiman yayi haka itama ta fara duban mijinta har a toilet ta dubashi bata ganshi ba cak ta tsaya da taga kofa a bude, a hankali ta fara tafiya ta nufaci kofar da zata kaita falo wani faduwar gaba taji da bugun zuciya tsallako kofar tayi ta nufo mijina kam ta kame tsaye akan matsanancin tashin hankalin da taji, mijinta dearest dinta ta gani a zaune da wasu kananan kayan da hula da wasu rufaffun takalma kai! Sak shigar USMAN! Yadda yake zama, yadda yake kada kafa daya juye hularda yake yi kai! Kome sak na MAN! Daga kai yayi ya fara dubanta tun daga sama har kasa, itama suban nashi takeyi, nikewa yayi kau!! Ya wanka mata wani hatsa bibin mari said a ta fadi ta fasa bakin ta, kamar wanda ya dawo daga hayyacinsa y ace cikin wata murya wadda ko ba’a gaya maka ba kasan mace c eke wannan murya,


yanzu idan Usman yaji yanda nayi miki fa ya fara dube-dube kamar wanda yaga usman din a falon, da karfi kuma ya juyo ya kalleta kallo irin na mugunta da tsananin kiyayya yaci gaba da Magana wannan dai ta mata, idan na kasha ki ai bai zai taba sani ba yana fadi yana cize hakoranshi, ya nufaci inda take ya sa hannun ya cafko wuyanta ya dagata dashi sama har ya cirata har karfi aka banko kofar shigowa falon! Tsohon nan ne da suka saba dashi, da karfi ya wankada mashin wasu ruwa da suke rike da hannunshi, wai gowa Sulaiman din yayi da karfi suka hada ido da tsohon, wurgarda Bilkisu yayi da karfi ya sheka ya nufi bangon falo tuma yayi ya tsunduma cikin bandon baya bace. Baban yaje ya tayadda ita kuka takeyi kamar ranta zai fita, ba dai Usman ne keyin duk wannan abinda ke faruwa ba, take fadi tana kuka mai tsanani. Ba Usman bane ke muku wanna abun amma sanadiyar sa ne duk wannan abun ke faruwa, how? Tayaya? Ina mijina kuma wane sanadine na Usman aka da yake faruwa dan haka ta fada tareda zubewa a kasa tana kuka. Gyara zama yayi ya fara fadi mata kamar haka ——–

Ku biyoni a littafi na biyu dan jin cigaban kayatacce labari.

Taku mai debe muku kewa Asiya Sadiq Maccido

(Asikhan)

Tel: +2349037433171

Anime girl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

error: Alert: Content is protected !!