Hubbul yaqeen series two

Shi kuwa Sulaiman bayanda mahaifinsa Alhaji Haliru ya isa gida, ya kira uwargidansa ‘ya shaida mata duk yanda sukayi da malam Iro, wato dangane da batun aurenda ya nemawa dansu Sulaiman, tun daga farko har karshe.Kamar yanda yake tsammani matarsa, mace mai kirki da biyayya wato Hajiya Aisha tayi na’am da wanna zancen dari bisa dari, da kanta tasa a ka kira Sulaiman kasancewar tun-tuni yana gida, da hanzarin sa ya isa a falo inda mahaifansa ke kiranshi, ya duka ya gaida mahaifinsa ya umurceshi daya nemi guri ya zauna bayan ya zauna ya fuskanci mahaifinsa, Sulaiman game da tafiyar da zakayi Kaduna ne, kasancewar an mayarda kai ga baki daya acan, a matsayinka na namiji, bai kamata ace kaje gari da zama kai kadai ba, wannan san ba mutncin bahaushe bane, bisa ga la’akari da wannan da kuma ma wasu dalilai da ban gayamaka, na yanke shawarar zanyi maka aure kaje da matarka acan.Ras!! gabanshi ya fadi kamar andoka masa guduwa a zuciya da kyar ya hadiyo yawon da suka makale masa. Bai samu ta fadi ba gyada kansa kawai yayi alamar ina saurarenka. Nayi Magana da mahaifin yarinyaarda zaka aura, na namar maka auren yar’sa ya kuma amince da haka, harma mun saka ranar bikin, nan da wata hudu masu zuwa, sai ka rika zuwa wurinta domin ku fahimci juna ko? caraf mahaifiyar tasa ta amshe zancen tare da fadin, can ne gidan Malam Iro yarsa Bilkisu itace surukar taa tana murmushi, ta kara da cewa kasan maigida akwaishi da iya zabe. Shima mahaifin nashi murmushin jin dadi yayi yace ka fahimce ni ai ko? Daga kanshi yayi da yake a duko yace eh Abba nagode Allah yasa haka shine mafi alkhairi, amen Sulaiman tashi ka tafi Allah yayi maka albarka, mikewa yayi tare da fadin amen ya fice da hanzari ya bar dakin, kan gadonshi ya nufa, bai tsaya wata-wata ba ya afka saman gadon nashi, shin me mahaifansa ke shirin yi masa? aure!!. Kamar Bilkisu shima kogon tunani ya fada. Shi dai baya zargin mahaifinsa akan abinda ya aikata masa, domin kuwa yasan Bilkisu yarinyar arziki ce mai hankali da natsuwa, amma kuma shi bai taba jin yana sonta ba.Juyawa yayi kan katifarsa yana sakawa a ransa, “idan ma bai amince da wannan al’amarin ba wace mace ce nake da da har zan kawo nace ina sonta”. Tunda yake bai taba fadawa a tarkon son ko wace “ya” mace ba domin kuwa shi burinsa daya ne a duniya ya zama cikakken dan sanda mai gaskiya da rikon amana, sam bai dauki soyayya da wani matsayi ba, shi a ganinsa zata zama kashin baya ne wajen ruguza masa burin sa. Runtse idanunsa yayi ya danyi tsaki, ba damuwa ai naji ance soyayya a hankali take shiga a cikin zuciya, kuma ma koda banajin ina sonta a cikin zuciyata, bana kuma jin bana sonta, Bilkisu yarinyace mai hankali gata kuwa da ilimi, don haka inada yakinin cewa insha Allah zanji dadin kasaan cewa da ita. A haka yaci gaba da sake-sake har bacci yayi awon gaba dashi. SHIN WANENE SULEIMAN? Sulaiman dai saurayine kyakkawa na gaban kwatance, dogo ne, fari tas irin kuwa farin larabawa, yanada saje, wanda ya kara fitar masa da kyan fuskarshi, ba domin wannan sunanshi Sulaiman ba kuma a Najeriya yake da idan ka kalli film din (student of the year) na indiyan nan, zaka zata tawaye ne da siddhart malhutra dayan saurian Alia batt wanda ya aure ta a fim din akan matsanancin kamar da suka yi dashi.Washe garin wannan rana da dare Sulaiman ya shirya cikin riga da wando kaftan jar shadda ce tasha gawado harta gaji hulah baka ya saka da takalma bakake, ya fesa turare dan ubansu, gaban (dressing Mirro) yatsaya, ya dau mintoci yana kallon kanshi, kana yayi murmushi yasa kai ya wuce. Dama shigarsa kenan, ga baki daya baya sanya kananan kaya ba wai domin yana gudun ko ba zasu yi masa kyau ba a’a sai domin shi kwata-kwata basa cikin tsarin rayuwarsa. A dai-dai kofar gidansu Bilkusu ya tsaya bai wani dade ba, ya hango yaro ya aikashi yaje yayi masa kiran Bilkisu, Bai fi minti goma da wucewar yaron ba. Bilkisu ta fito, kanshi na a duke yana dannar wayarda ke rike a hannunsa, wani kamshin turare yaji mai matukar kanshi ya doki hancinsa, daga kanshi yayi, yayi arba da kykkyawar fuskar Bilkisu abin kamar hadin baki itama jan kaya ta saka duk da batayi wata kwalliya ba tayi matukar kyawo, ya yadade yana ganin Bilkisu unguwarsu daya tun tana karama har ya zuwa yanzu data girma amma bai tabajin tayi masa kwarjini ba sai a yau. Sallama tayi ya amsa mata ta gaidashi, har yanzu bata kalleshi ba, lafiya kalau yasu Umma, sai a wannan karon ta daga kanta ta kalleshi dam! taji gabanta ya fadi batareda tasan dalilin faruwar hakan ba, Gaskiya shigarshi ta burge ta tanason namiji mai shiga irinta kamala, tasha gwagwarmaya da Usman dinta akan ya rika saka manyan kaya, amma shi ba kamar Sulaiman ba yafi son kananan kaya duk da can ba’a rasaba yakansa manyan kaya ya gwammace yasanya kananan kaya na naira dubu goma riga da wando kawai sunfi mishi akan ya sanya shaddar dubu biyar. Amma kuma halinsu sam ba dayaba shi Usman yarone dan kwalisa mai cike da takama da nuna isa, sabanin shi Sulaiman da kwata-kwata wannan bai dame shi ba, sunyi firarsu irinta masu hali iri daya, kowa ba gwani bane wajen iya sarrafa harshe da zuba zance, sai dai abinda ya burge su dukan kasancewar kusan halayensu ma duka iri daya ne, kuma su dukansu sun kai matuka wajen iya mutanta juna, a haka suka yi bankwana suka watse tare da musanyar lambobin wayar juna.Sannu a hankali suka rika sabawa da junansu har ta kai daya baya so yayi kwana biyu ba tareda yaga dan uwansa ba.Sun shaku matuka a cikin yan kwana kinda sukayi har ta kai ga kowannen su yana shakkar zuciyarsa akan cewa anya! ba son dan uwansa yakeyi ba? Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a dade ba’a kai ba, masu iya Magana kance lokaci abokin tafiya wanda baya jiran kowa.A yau ne aka daura auren Sulaiman Haliru Moh’d da Bilkisu Ibrahim Khalil. Anyi biki an kuma tofa Fatiha an kai amarya dakin angonta, su Asiya baki baya rufewa kawarta tayi aure.Wannan rana itace rana mai matukar muhimmanci a garesu domin kuwa sun cimma wani matsayi na Rayuwa. Salamu alaiki ango ne ya shigo dakin amaryarsa mai kamshi da sheki kamar wata zinariya, tashi sukayi, sukayi raka’a biyu kamar yadda shugaban Halitta ya umurta, suka nemi Allah ya sanya Albarka da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin su. Zaune suke da junansu lafiya bakajin tsakaninsu, hakika su karan kansu sun san sun shiga cikin wata duniya, wannan kuwa ba ko wace duniya bace face duniyar soyayya da tsananin begen juna. Satinsu daya a garinsu wato Bauchi suka gangami nasu ya nasu suka cilla ya zuwa Kaduna inda aka tura Sulaiman da aiki.Bilkisu taci kuka kamar ba gobe, gani take kamar ba zata dawo ba dakyar ango ya iya shawo kanta ta hakura dole, sun sauka ne a wani hotel anan cikin garin Kadunar, kasancewar sai dare suka sauka. Washe gari Sulaiman yaje ya nemo musu gidan haya.Da fara’ar sa ya gayawa Juliet dinshi sun samu gida mai kyau dai-dai su kuma yana da tabbacin zata so gidan matuka, abinda ma yafi burgeshi da gidan shine irin (self content) dinnan ne wanda komai akwai ciki,su gado,kujeri, katifa kai komai ma akwai aciki. Itama Bilkisu ba karamar murna da farinciki tayi ba tun kan ma taga gidan.Sai yanzu Bilkisu ta tabbatar da abinda mijinta yace gaskiya gidan yayi sosai. Da isarsu basu tsaya wata-wata ba suka fara aikin gyara gida baji ba gani duk da yake Sulaiman ya samo musu wa’yanda zasu taimaka musu da aikin.Bayan sun kamala gyara komai, Sulaiman ya biya wa’yanda ya dauko domin su tayasu gyaran gidan. Gida yayi kyau matuqa gwanin ban sha’awa da shi ko’ina ka duba kyal-kyal kawai yake kasancewar tiles (tayis) ne fari sol dukan gidan mai kyan gaske ne. Farkon gidan wani gate ne mai qayatarwa, idan kuwa ka shigo cikin kitchen. Gaba kuwa idan ka fito tsakiyar falon gabas da falon bedroom kenan wanda yake dauke da matattakalai guda biyu kafin ka shiga, bima’ana kofar nada dan tsawo kadan, a cikin bedroom din kuwa akwai toilet. Duka wayannan dakunan wuri daya suke, sai dai kuma wani dan wuri da akayi kamar wurin wanke-wanke, dan korido ne akayi mai dan tsawo. Idan ka shiga cikin wurin zaka hadu da wani daki a can karshe wanda ga dukan alama (Store) ne, a gefenshi ne akayi wurin wanke-wanke tareda fanfo da kuma inda ruwa zai fita waje, ya fada cikin (Suck-Away), kai a gaskiya gidan yayi matuka. Bayanda suka kare gyara, Sulaiman ya tafi ya siyo musu abinda zasu ci da kuma kayan abinci ma’ana (Provision). Fitarsa keda wuya ta dawo falo ta dan kwanta saman kujera ta kishingida akan doguwar kujera. A hankali aka fara jan kujerar da take kai, ta yanda ba za’a tada ta daga baccin da takeyi ba, daga bisani kuwa kujerar ta daga sama chak da ita batare da wani bil’adama ya dauketa ba, ita dai kujerar da kanta ta cira kanta da kasa ta nufaci kofar falon, adai-dai wurin ta ajiye kanta. Sannu a hankali harta kai a kasa, ba tareda Bilkisu ta koda motsa ba. Sulaiman ne ya dawo,bude kofar da zaiyi sai yaji kamar wani abu ya danne kofar,iza kofar ya sakeyi amma a wannan karon da duka iya karfinsa, aiko sai ga Bilkisu a kasa rim!.Da saurinsa ya shigo a falon ya taimaka mata ta tashi. Har goshinta ya fashe da jini, sakamakon tayis dake wurin kuma ba kadan ta fadi ba. Meya kawoki a nan Bilkisu, Sulaiman ne ya fada yana mai cike da matukar mamaki.Itama dai Bilkisun rasa ta cewa tayi, tsananin mamaki da al’ajabi ya dabaibayeta. Sai can ta samu tace nima bansan yanda akayi nazo……….. bata samu damar ida maganar da takeyi ba Sulaiman ya fashe da dariya key’ an mata ki fadi gaskiya, ke dai kinga ba kowa a gidan sai kikaji tsoro shine kika janyo kujera, kika kawo bakin kofar falo kina gadi, kafin ayi haka bacci ya kwasheki. Yaci gaba da dariyarsa batare da ya lura ta bashi ansa ba, murmushin yake kawai tayi tace to naji tunda haka kace.Amma har a zuciyarta tasan ba hakan bane, tasan ba anna ta kwanta ba, lallai wanna abin da ban mamaki yake, ita inama take iya daukan wannan kujera mai matukar nauyi, amma nan a take ta share da maganar a ranta, ta karbi kayanda Sulaiman ya siyo, shima kuwa ya taimaka mata wurin aje ko wane abinci inda ya dace. Lebara ya samu suka shigo da sauran kayan abincin sannan suka mayarda kujerar mahallinta na da. Bayan sun kammala cin abincin daya siyo musu, suka dan kunna kallo farin wata (T.V) suka sa amma kwatakwata hankalinsu baya kan kallon.Hira suke abin gwanin ban sha’awa. Bilkisu kinga gida yayi ko? Eh wallahi abin sam barka, naji mamakin yadda muka sami gidan nan acikin farashi mai sauki haka, sai kace dai kyauta aka bamu. Murmushi yayi yace nima dai abinda na gani kenan, mutumin yayi muna rangwame sosai, kuma fa duba duk da kayan nan dake ciki bankara da yadda na gaya mikiba. Nima fah (Dearest) kaga abinda ya qara burgeni kenan, mutumin ya yi muna rangwame sosai wai ashe dama ana haka, abawa mutum hayar gida harda kayan dake ciki? Dariya ya farayi kafin nan ya bata ansa, ke malama ba wai harda kayan duk haya bane, kayan. Duk Month zan riqa bada wani abu har in biya ga baki daya, kinga kenan sun zama namu.. Oho! Yanzu na fahimta itama ta danyi dariya. Duba agogon dake jikin bango yayi kai ashe dare yayi itama dagowa tayi ta gani ai kuwa.To bari naje na kwanta kinsan gobe zan koma kan aikina. Nasan kuwa ke sha daya da rabi ake fara series dinda kike so ko? Don haka na barki lafiya. Mikewa tayi itama. Ka manta ai yau Lahadi, basa kuwa yi ranar weekend sai gobe. Kwarai kuwa hakane kinga harna manta Wurin kayan kallon ta nufa ta kashe sannan tabishi suka wuce bedroom suka kwanta. Da asuba Sulaiman ya fara tashi kasancewar dama ita Bilkisu a gajiye take kan gyaran gidan da sukayi. Sai da ya fara shiga toilet ya dora alwala sannan ya tayarda ita domin itama tayi sallah daga bisani ya wuce masallaci tashi tayi tayi alwala tayi Sallah ta fada kicin tayi musu (break fast) koda tafito Sulaiman ya dawo sai ta kwaso abincin ta kawo dani taje ta gaida shi da kwana sannan ta gaya masa ga ( break fast) nan (ready). Tasowa yayi suka dunguma sai (dany) sukayi kari lafiya qalau ta dauki kwanuka taje ta wanke ta fara wankan kwanukan kenan a dai-dai farkon korido taji kamar mutum ya tsaya yana kallonta irin kaji nauyin mutum hakannan. Juyawar da zatayi sai taga ba kowa ta danyi shiru kadan kamar mai nazari sai kuma ta juya taci gaba da wanke-wankenta sake jin tayi mutum a bayanta a wannan karon ba’a tsaya a farkon koridon ba, da karfi ta juya kuma sai taga ba kowa, tattara kwanukan tayi duka zata juya ta waiga sai kawai taji nauyin mutum gaf da ita da azama ta wuce da karfin tsiya dogon numfashi taja da ta ga sulaiman ne tsaye yake kallon ta a wannan karon lafiya dai naga kamar a firgice kike? Lafiya qalau ta fada tana mai dan yin murmushi. Zoki dan taimakamin ki gogemin takalmana please kinsan sauri nake karna makara ta kammala goge masa takalma a dai-dai lokacin da ya gama sanya (uniform) dinshi karbawa ya yi ya sanya tare da fadar (thanks you) ya kika ganni yayi tsaye yana kallonta, kayi kyau sosai Sir! tare da sare masa, dariya sukayi su duka. Ta rakashi ya wuce ita kuwa ta dawo. Ta kunna kallo ta zauna a falo abinta. Ba’a jima ba ta tashi taje tayi musu abinci, tayi wanka ta dawo falo taci gaba da kallo (Rimote) ta jawo ta canja tasha zuwa Zee cinema inda tayi sa’a ana bugun number fara wani film kenan. Kallo takeyi gaba dayan hankalinta yana kan (T.V) sai gani tayi wani bakin fata ya taso ya rufe camera gabaki daya to me yakawo bakin mutum a Indian Film kuma Ita dai tunda tafara kallo bata ga an nuna shiba sai yanzu kuwa gashi yazo ya rufe t.v ga baki daya shi ka dai ake gani.Ke! da karfi bakin mutumin ya fada. Ke kuma a Indian film din? Ke! Dake fah nike yi, bude idanu tayi gwala-gwala tana kallon ikon Allah. Ke!! ya daka tsawa har sai da ta zabura ke maigado dake akeyi ko ke kurma ce, da karfi ta tashi tana mai ja da baya-baya. Don Allah malama kije ki budewa mai gidanki gashinan shigo—– bata jira ya idar ba ta yanka da gudu tsoro taji na fitar arziki da karfi ta bude kofa da nufin gudu aiko nan taji kafarta ta juye sai fadawa tayi kan wani abu a hankali ta bude idanuwanta mijinta Sulaiman ta gani lafiya lafiya? Bilkisu meya faru kika sheko haka me ya biyoki ne kuka ta farayi Zee cinema ……. Ta kasa fadin kome kara fashewa tayi da matsanancin kuka da kyar ta yadda suka shiga cikin Falo. Abin mamaki kuwa kayan kallo ma a kashe suke yaje ya zaunarda ita akan kujera ya bude firji ya dauko mata ruwa masu sanyi ya bata kuka kawai takeyi da kyar ya samu tasha sannan ya zauna a kusa da ita yana mai lallashinta da kyar da sidin goshi ya samu tayi shiru ta daina kuka ya tambayeta miya faru ta kwashe labari ta gaya masa. Kamar almara yaji abin amma da yaga taji tsoro matuka sai ya kanne bai nuna ba, addua’a yayi ya tofa mata akai sannan yace a duk sanda taji tsoro ba kuka zatayiba ta ringa fadar la ilaha illa antas subuhanaka inni kuntu mai nazzalimin, da kuma Ayatul kursiyyu ba komi bane face shedan yakeso yayi wasa da hankalinki, ki rike addu’a insha Allahu bake ba sake jin wani tsoro a gidannan. Ta dan samu kwanciyar hankali sannan yace taje ta samu bacci sannan ya fito Falo ya dibi abinci da kanshi yaci. Tun daga wannan rana ta riqe addu’oi baji ba gani duk da yake wani Sa’i takanji kamar an tsaya mata akai ko kuma taji kamar idan tana tafiya ana binta a baya ko taji an wulgo da karfi haka dai abubuwa suka ci gaba da faruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

error: Alert: Content is protected !!