HUBBUL YAQEEN SERIES Three

Suna zaman su lafiya da Sulaiman abin sai ace san barka. Misalin karfe sha daya na dare yaji ana tadashi daga barci buda ido yayi, me zai gani farin cikin rayuwarsa ce Bilkisu a tsaye taci ado da wadansu kananan kaya masu jan hankali, tasha kwalliya ta fitar hankali sai kamshi takeyi mai matsanancin dadi tsaye take tanayi masa wani mayen kallo ai kuwa bai san sa’ada ya tashi zumbur ya mike ba, ta dan ja baya kadan ta bude hannuwanta biyu alamar yazo, saikuwa yayi kai tsaye inda take amma sai ta goce tana mai yi masa dariya. Au ni zaki wasawa haka da gudu ya bita suka fada sai a falo da gadunshi a tsaye yayi chak—– sakamakon ganin Bilkisun shi zaune a falo tana kallon Series dinda take kallo ko yaushe mai makon tufafin da ya biyota dasu kuwa rigar baccin da yasan Balkisu da ita itace sanye a a jikinta da saurinta ta mike da sauri lafiya dearest me ya faru naga ka shigo haka da gudu lafiya. Bai samu ta cewa komai ba mamakin ya hanashi Magana ga baki daya sai a ranshi yake Magana ba yanzu na biyo Bilkisu da gudu ba, idan dai ga Bilkisu nan a zaune to waccan wacece na biyo kafin ya samu amsar wadannan tambayoyi na Bilkisu, ta sake tambayarsa lafiya baka ce komai ba, menene? Murmushin yake yayi yace babu komai amma da yaga Bilkisu na tantamar abinda ya fada sai yace mafarki yayi wai tana nakuda akace ya sheka ya kira likita shine ya shigo wai, dauka ta gaskiya ne. fashewa tayi da dariya tare da ajiyar zuciya dauke indonta tayi akan nashi yanzu dan wannan gudunne zakayi in akace ka kira likita? Dariya kawai yayi batare da ya bata amsa ba, zuwa yayi ya kashe kayan kallon, chak ya dauketa, dama dariyar takeyi harda ma shakewa, Malama (is time for bed now), sai daki ya ajiyeta ya maida kofa ya rufe.


Gobe (workers day) kamar kullum ma’aikata suna hutu, Sulaiman tunda safe yasa Bilkisun shi tayi musu girki mai dan yawa yaje ya dauko motar ofishinsu ya dauke ta sai babban (park) din kaduna sun yi nishadi sosai. A can basu wani dade da zuwa ba, yace bari ya daukota su zaga gari domin taga Kaduna tunda yau (free) yake a cewarsa yau wata babbar damace daya samu, anan take kuwa Bilkisu ta amince da wannan shwarar, sun zazzagaya wurare da dama balkisu ta bude ido, a gaskiya Kaduna babban birni ne mai kyan gaske. Bari muje bakin ruwa ko Balkisu? Da hanzari ta amsa masa da eh muje, dama kamar yasan abinda yake rantane ba abinda Balkisu keso daya wuce wurin ruwa. Tafiya suke kowane ranshi cike da farin ciki, ‘yar fira suke gwanin ban sha’awa. “Wai ni ko in tambaye ka mana” Balkisu ta fada tare da kallon Sulaiman, eh ina saurarenki yace batare da ya kalleta ba kasancewa driving dinda yakeyi, halama dai baka son zama cikin mutane ne? Me yasa kike fadi haka? Sulaiman tare da yi mata wani kallo mai dauka da alamar tambaya kawai dai naga daka tashi nema mana gida ne sai ka nemi layin daba mutane a cikin sa mutane saura duk irin gidajen nan ne na manyan yan siyasa da suka yi domin kawai idan sun shaqi iska suzo suyi dan hutun sati biyu su koma ni ma tunda nazo duka gidajen da ke side dinmu masu gidan ko sau daya basu taba zuwa ba, sai kuma sau daya gidan da muke (facing) suka zo suma basufi (two weeks) ba suka wuce, su kuma gidajen nan hudu da suke akwai mutane aciki uku duk (cristian) ne fah. dayan kawai ne musulmai su Khadija da Fatima kuma suma bawai kusa da gidanmu suke ba. Hakane amma ba yanda kike nufi bane, me zai/sa na ki son zama acikin mutane bayan cikin mutane na tashi, Allah dai ya nufa nan zamu zauna shi yasa, kuma banda abinki ba gani ba koda bamuda maqota ai kullum ina tare dake kamar inuwa ya fada tare da murmushi itama murmushin tayi, hakane (Dear) af dazu ko na manta na gayama Umma ta kira tace na gaisheka, ina amsawa ko mutanen gidan ina fatar kowa lafiya,  lafiya qalau, madallah,, Bilkisu mun iso, a dai-dai lokacin da suka iso wurin ruwa yayi parking ya fito ya budewa Bilkisu itama ta fito tare da fadin (thank u) bude boot din mota yayi yafito musu da babban (carpet), ita kuwa Bilkisu ta bude sit din baya ta dauko abinci wuri suka nema mai ni’ima suka shinfida suka zauna, bilkisu ta dibar masu abinci suka ci, kasan garin Kaduna baban birni ne dab a wanda ya kula da wani, bayan sun kamala cin abinci suka dan taba hira irinta miji da mata suna tsakiyar firar ce Sulaiman ya hangi mai sayadda Tuffa wato (Apple), Bilkisu bari naje na siyo mana apple yanzu na dawo, ya tashi ya nufi wurin wai sayadda Apple, kai mai Apple nawa Apple, din, ya sayi apple din ya miqa masa kudi ya jira shi ya bashi canji, juyowar da zaiyi ya dubi gurinda Bilkisu take, me zai gani ya gani wata mata sani dai-dai sa’ar Bilkisu ta rige Balkisu a tsakiyar ruwa tana nutsar da kanta da gudu ya rugu ya watsar da (Apples) dinda ya siyo Bilkisu!Bilkisu! gudun yake yana kiran sunanta, ita kuwa wannan matar a dai-dai lokacin ta nutsar da ita gamin da tsoma kanta cikin ruwa Bilkisu nata kokari amma a wanna karon sai ganin yayi kafafuwanta dake motsi sun daina, har yanzu matsanancin dugu yakeyi yana kiran sunan Bilkisu, bai Ankara ba sai ji yayi tuntube sai kasa ya fadi ya wuntsila duk da haka mikewa yayi da sauri ya sake ruga wa. Ga baki daya mutanene da ke wurin kallan sa suke yi, ji yayi, kamar daga sama murayan Balkisu a bayan shi, bai fasa gudunda yake yi ba, ya dan juyo kadan, me zai gani Balkisu ce kuwa take binsa da gudu tana kiran sunan sa tsaye yayi duba cikin ruwa yayi a inda yaga wata tana kokarin kashe masa Balkisu shi, ba kowa wurin lokacinda ya juyo inda Balkisu ke gudu tana kiranshi, har balkisu ma ta karaso idonta cike da kwallah ganin irin mummunan faduwar da yayi, da zuwa rungume shi tayi ta fashe da kuka lafiya Dearest mike faruwa gani ana, ina inda ka barni banje ko inaba meke faruwa? da kyar ya hada yawu da suka lake masa, numfashi yake sama-sama Alhamdulillahi Balkisu tunda kina lafiya ba abinda ya sameki, dauko kaya mu wuce yanzu-yanzun nan kasa Magana yayi, ga baki daya mai Apple ne ya iso bakin mota, Alhaji ga canjin ka fa da Apple din da ka saya, said a Sulaiman ya dan tsaya kamar mai nazari sanna ya ansa, ya wuce ya bude mota ya tada suka wuce gida, ba wanda yake Magana a cikinsu.


Ita Bilkisu tunanin ta keyin ya akayi mutum ya barta zaune sanna ya dawo a guje yana kiran sunanta har da wannan irin faduwa haka? wadda tayi sanadiyar daya fasa. Hancin sada jinni mike damin Dearest dinta me ya gani ne haka lallai koma meye ba lafiya ba, amma ba yanzu ya dace tayi masa Magana ba kamata yayi ta bari sai sun iso gida hankalinshi ya kwanta sannan, domin yanzu yana cikin rudu da fargaba. Shi kuwa a bangaren Sulaimn ga baki daya kansa ya kwance stabbas yaga wata tana yunkurin kasha balkisu yasan lallai yaga haka to amma kuma ya akayi bayan da ya sake dubawa yaga ba hakanan bane, idan dai balkisu na can a inda ya barta da yaje sayen Apple to waccan da ya gani wace? Wacce wadda kuma ta yi yunkurin kashe waccan Balkisu? anser day a kasa ganewa kenan har ya iso gida bayan ya shiga ya bude gate ya shiga da mota ya kulle gate ya dawo, ya taradda Bilkisu na jiranshi a kofa suka shiga taje, kai tsaye ta dauko first aid box ta bashi taimakon gaggawa, taje ta mayar da magungunan ta kuma biyo mashi da ruwan sanyi, ya ansa yasha, bayan kamar minti biyar ba wanda yace uffan sai Bilkisu ta katse shirun da tambayar shi ko lafiya game da abinda ya faru dazu? Ya so ya gaya mata sai kuma ya tuno da cewa Balkisu mace ce idan ya fada mata zai kara dagula lissafi ne kawai. Domin haka yace ta barshi ba komai bane amma sam taki amincewa da haka, da dai yaga tanace akan sai ya fada mata sai ya maida abin ba’a yace yana ganin sonta ne yake neman zautar dashi, duk da ta san ba haka bane ama sai murmushi ta sharer da maganar kamar yadda. Taga baya son zancen, tun daga wannan lokacin bata sake tamabayarshi ba kuma, yayi kamar sati baya wani sakewa sosai ko office yaje zai yita kiranta yaji ko lafiya, amma sannu a hankali anaka manata da wannan abu komai ya dawo normal a kaci gaba da yadda aka saba, yau asabar su Balkisu sukayi baki abokanshi Nuhu dashi da matarshi a gidansu, suke wuni sai bayan magariba suka wuce tare da alkwarin suma wani sa’I zasu je suyi masu yini kamar suma yadda suke yi masu. Bayan wuce war su Nuhu Sulaiman yasa Balkisu tad an dafa masa abinda zasu ci domin ba sauran abinci a gidan kasancewar bakin da sukayi sunada zara, kitchen ta shiga ta daura abinci macaroni ce yar two minute ta aza musu, ta dauko timatir fresh tana yankawa harma ta kusa kareyankawar, daya kawai yayi saura maid an girma haka, yanka wanda zatayi sai kawai taga jinni ya fito cikin tumatirin, sake dubawa tayi kamar dai wadda ta tashi daga mafarki. Tabbas haka dinne jinni ke zuba daga jikin tumatirinda ta yanka, baya-baya ta farayi tana duba ttimatirin me zata gani saurantimatirin data yanaka ga baki daya wasu irin tsutsoci ne ke fitowa daga garesu ta ko ina kara yi tayi da baya tana shirin guduwa sai kawai tayi kicibis da Sulaiman, lafiya? A firgice sai juyawa tayi tana nuna timatir din. Me ya faru yankewa kikayi wajen yanke timatirin ko shiru tayi ta kasa cewa kome a, sakakamakon ganin timatirin da tayi lafiya kalau ba abinda ya same shi, ba wani jinni bare kuma wasu tsutsoci dake sukuwar sallah a sama a.a da rasa ta fada tayi to meyee haka? mike faruwa ne day a dauki tumatitrin abinda take fada bay a dauki tumatirin da kanshi yasa cikin tukunya ya juya kinga jeki zauna yau zakici girki mai dadin da baki saba cin irinshi ba, kasa tafiya tayi saida yazo ya fitar da ita da kanshi Sulaiman ne yayi masu sanwa sam bata iya cin abincin da kyarya matsa mata ta danci kadan, abincin ba, ku fa mata haka kuke idan kamala shirin ba, ku fa mata haka kuke idan dai mutum yace ya jira ku to shi kuwa sai ya shiga uku da jira Sulaiman ya yakema Bilkisu bita, na kare ranak ya dake muje ta fada tana dariya tare suka fita suka kulle gida ya dauketa wurin saloon suka, nufa can kan titin shigowa layin su. Sai a bakin shagon ya ajeta tare da bata kudin saloon din har ma da Karin, idan aka kare sai ki kirani sinzo na mai dake gida murmushi tayi tareda fadin nan wurin ne har sai ka dawo daga office dinku ka mayarda ni sanna ka koma? Malam ko cikin dare ne ai zan iya mayadda kaina ballantana zanzu da rana kiri-kiri.


Shima murmushi yayi yace to kinga laifina ne ina tsoron kada ki bata ne kinsan Kaduna da fadi idan kika bata a in azan nemoki, har ganoni ne wani abin wahala ni ai ko a brining sin ka bat azan nemoka, ke kin kuwa san ko inane birnin sin kinsan yawan mutanen da ke cikinta, Dearest bari ta yawan mutane ko a Birnin ALJANU DA FATALWA ka bata wallahi ni Blkisu sai na nemoka koda kuwa zan rasa rayuwata ne. wani irin dadi Sulaiman yaji musamman da yayji irin tsantsar kaunar da Balkisun shi take mishi, allah ko matata? Ya tambaya yana main zolayanta ko shakka babu ta fada tare da taba kundar ta suduka suka fashe da dariya, to bari na wuce office kar naje na dade na bata nasa matata cikin wahalar nemana, sake fashewa sukayi da dariya ya tada mashin dinshi bye love ya fada tare da kashe mata ido daya murmushi tayi see you soon ta sfada ta kuma hanyar shiga cikin shagon saloon din, sai da ta shiga cikin shagon sanna ta juyo shima Sulaiman a dai-dai lokacin ya juyo suka hada ido dariya yayi ya daga mata hannu alaman bye bye sanna ya juya yaci gaba da tukin mashin dinda yake yi, murmushi kawai tayi ta karasa shiga cikin shagon excuse wata mata ta amsa da yes shigo. Sannu fa ga wuri ki zauna ta zauna, ta zauna tareda fadin nagde me kikeso ne madam inji mai shagon saloon sdin nazo sa mai ne okey bada bata lokaci ba ta fara cikinta shigar Bilkisu drayer kada wuya sai ga wata syarinya yar kimanin shekara sa takwas ta shigo a cikin shagon da gani basai ka tambaya ba kasan ‘yar mai shgon ce domin tsananin kamarsu day abaci said a ta gaida Balkisu sannan ta koma kan maaifiyarta dauke take da kwan abinci da kuma wani jug da drinks aciki, mummy ga abincin na qare ni zan koma shagon, wani dan karamin siket ne iya gwaiwa tasa duk ilahirin jikinta a fili kai gaskiya ya musulunci nada dadi shine addinin dake mutunta ‘ya mace ya kare darajar ta da martabarta. Ita dai madam abincin wanda ke nuni da da cewa dama a jiraye, take malama muna kwarya fa please kici abinci a’a nagode wallahi, kici kawai ni a koshenake kallon abincin tayi, ta kasa gano ainihin menene kamar soyayyar doya amma kuma abin ya banbanta to meye haka gwanin ban sha’awa, taso tayi shuru sai kuma ta tuna matambayi baya bata kuma ma ai karuwanta ne, madam menene haka kamar soyeyyar doya domin saloon shi zanyiba, irin na soyayyar doyar doya bace. Haka ne wannan ba doya ta mikawa Balkisu kici kiji yanda yake yafi doya soyyaya dadi sossai da kyar balkisu taci aiko gaskiyarta gaskiya abinnan nada dadi sosai ya akeyin shi ne Madam. Bata jira ta kammala cin abincinta ba ta fara gayamata farko zaki dan dafa doyanki amma kada ya dafu sosai, kamar irin far-builing dinta tattasai da albasa, sai kuma ki fasa kwanki kisa spices dinki ki gurje, doya da kika sauke kuwa sai ki gujeta kaman yanda kike gurje yakuwa, ba wai yayi gari ba kinsan bata wani dafu ba, bayan kin gama gogewa sai ki zuba tarugunki da tattasai da kika daka tun farko ki gauraya ko’ina yaji, ji dan kara species dinki bada yawa ba sai ki kawo kwanki ki zuba ciki, shine ki gauyraya, sai ki samu leda kisa kamar dai yadda akeyi alala ki kulle ba sosai ba sai ki saka a ruwa zafi kamar zakiyi alala idan yayi da kin duba zaki gane, sai ki fitar kiyi masa shape din da kike so. Great gaskiya nagode, fah madam na karu sosai thank you onces a gain Bilkisu ce ta fada, madam kuwa sai faman budar baki takeyi itafa nan ganin yake ta burge. Sosai, no ai wannan is notting, shiru tayi kamar wadda ta tuna wani abu sai kawai ta tsayyoma drinks dinda yake cikin jug Balkisu ta kawowa malama ga wannan kisha ‘yar gajeruwar dariya balkisu tasa a’a gaskiya ki barshi kawai nagode ko wancan dana ci domin nasan ya dafuwanshi yake idan na dafa ne ki barshi nagode Allah. Malama Balkisu meyasa nace kisha ba ko wannan drinks din hadashi akayi kuma yanada dadi, sosai nasan mai gidanki zai so shi sossai shiru Balkisu tayi cikin ranta tana dariyar madam domin tasan wannan ba komai bane face dadin yabon da tayi Balkisu tayi mata, zugata da  taji anyi duk shi ya janyo takeso ta kara nunawa Balkisu ita ce kwaruwa ce wujen iya girke-girke. Karba kofi kawai tayi ba tareda tasha ba drinks din menene na cocumber ne da kwakwa a lokacin ta dan ka baki ta kurba kai? Gaskiya shima ya hadu. Cocumber da kwakwa shi kuwa ya ya akeyin shi, ai madam bata jira ta kammala maganar da takeyiba ta soma; farko ki fere cocumber ki sai ki yayyanka ki saka a bander ki blende ta sai ta blendu. Sosai sai  ki kawo kwakwa itama ki blader ta cikin cocumber idan kuma kin gama kina iya blande su tare, sai ki saka madara a ciki kisa cikin frige shikenan kin hada drinks dinki, kuma wani abin burgewa das hi drink dinnan bawai kawai dadin shi kesa ayi shi ba a’a yanada matukar amfani a jiki sossai. Gaskiya madam nagode sosai naji dadin zuwa saloon wurinki domin na karu da abubauwa sosai, kinga yanzu ko kina karemun gyara kai na zanje nayi abubuwannan da kika koyamin sauri karemin naje so drink suka fashe da dariya, madam ko ta gyara mata Kanata fes-fes gwanin ban sha’awar har bakin shago ta rakayota sukayi bankwana Balkisu ta wuce. Bata zame a ko’ina ba sai gidan su khadija da Fatima yan layinsu can ta nufa tayi kwatanta mata inda ake sayerda kwa-kwa domin duk abinda zatayi aiki dashi tanada kwa-kwace kawai batada, tayi kokarin kiran Sulaiman a waya Switchup tana sane ta gayamai zataje wani wuri ba zata dade da text, Sulaiman  dinne yake gayamata zai kai dare kada ta jirashi akwai meeting dinda zasuji ne kuma ba dole zai kasha wayanshi sauke nunfashi kawai tayi kutsa kai gidan su Khadija da Sallamarta Fatima kadai ta cimma Khadija batanan ta fita anguwa, tayi sa’a yar cikinsu Habiba nanan kuwa, ita ta aika ta siyomata,, ita kuma ta koma gida, kai tsaye ta nufi daki ta saukar da akwatuna gaba daya ta bude ta kasan sai data fitarda rabin kayan sanna ta kai ga wasu tulin kanan kaya ma’aita English wears, said a tad an tsya zabe sanna ta ciro wasu jajayen sun hadu matuka murmushi ta saki, lallai aminiyarta gwaruwace duk ita ta saya mata kananan kayan nan dama a inda ta dialiara kenan Asikhan? Asikhan ta fada tana dariya ta tuna irin mitarda tayi mata game da kayannan data saya mata, da gaskiyar aminiyartata duk cikin kayan ba Wanda bai kai matuka ba wurin kyau, kai wai ita Asikhan tana da kayanda tabawa muhimmanci ne da suka wuce kananan kaya? Dariya kawai tayi ta ajiye wadanda ta ciro Akan gado ta shiga mayadda sauran kaya ta maida akwatuna yadda suke, sannan ta fara gyaran gida ta shiga aiki tukuru baji ba gani tad an canga wasu kuwa duka ta maidasu falo ta bubbuga, komi yayi gwani ban sha’a. daganan kuma ta fada kitchien ta fara ferewn doya kenan taji bugun kofa da sauri ta nufaci kofa koda ta bude Habiba ta gani da abinda ta aiketa ansawa tayi, ta kuma yi mata godiya Habiba ta miko mata sauran canji naira talatin ne suka rage ki barshi kawai ki dauka na bakai in kinje kice ina gadasu kinji nagode Habiba tace tareda washe baki zasuji nagode Amarya ta sake fada, murmushi kawai balkisu tayi ta rufe kofa ta koma bakin aiki bata manta ba yadda madam ta gayamata haka tayi, kamar ko ba ranar ta farayi ba domin tayi dai-dai yadda akeso koma tayi kyau sosai ta fidda shape dinda takeso ta rufe a kula ta kai dany ta hada drinks dinta a hakikanin gaskiya yau ta aikatu, ta kamala hada drinks dinne a kayi kiran magariba, ta saka shi afrige ta shiga bandaki ta doro alwala ayi sallah, bayan ta idar da sallah ta koma kitchen ta wanke kwanukan da tayi aiki dasu ta goge kitchen din, sannan ta nufi frige ta dauko kankara ta faffasa ta saka ta sake mayadda drinks din a cikin frige, kiran salla isha’I taji taje tayi sallah, ta cire kayanta ta nufi bathroom har takai kofar shiga toilet din kuma sai wani abu ya fado mata a rai, falo ta nufa ta bude kofar falon tad an iza kofar ta yadda idan mutum ya iso daya dan tura kofar zata bude sannan ta nufi daki ta rufe kofar dakin amma a wannan karon dakin kalloshi tayi ta yanda idan dai ba ita da take ciki ba ba wanda zai iya budewa, dariya ta saka sanna ta fada toilet tayi wanka abinta bayan ta kamala wankan a gaba dressing mirrow ta tsaya, tunanin irin kwalliyar da takeyi sanna ta zauna ta fara zuba kwalliya bata kammala kwaliyarada takeyi ba can a falo taji sllama dearest dinta, salamu alaikum Honey in Home ya kara fada dariya kawai tayi, tace gaba da kwalliyarda takeyi, kai waye daki ya nufa wai ina masu gidanne, za kofar dakin yayi ya kuwa jita gam a kulle, a,a Balkisu lafiya dariya ta sake sakawa malam kaje falo ka zauna zan fito nan da minti biyu shiru yayi duk mamaki ya cika shi as you wish my lady na fada ya komo falo ya zauna, sai kamshi kawai ya keji yana tashi, dama ko yunwa yakeji, ita kuwa Bilkisu saka kayanta takeyi ta bude yar karamar kit ta dauko agogo ja ta saka ta sake komawa a gaban dressing mirow ta kalli kanta masha Allah ita karan Kanata tasan ba karamin kyau tayi ba, hakika aminiyar tat a cancanci yabo wayanna kayan haka, wana murmushi ta sake, ta jayo turaruka kala-kala a fara yiwa kanta wanka dasu bancin na jikinda ta shafa kafin ta saka kayan kanshi ba’a cewa komai, kofa ta nufa ta bude a hankali sannanta leka wata yagogan mata ya kasa hakuri harya isa diny ya fara bude kula fitowa tayi ta tsaya ajikin kofar nade kafafuwanta tayi ta aza daya bisa daya sannan ta jigina a kan kofar hannunta kuwa dagashi tayi sama ta mannashi da bango, irin tsayinnan dai tayi nay aka gannine, irin wanda karishna kapoor tayi a cikin film din raja Hindustani wani kamshi ta doki hancin Sulaiman a yayinda yake kokarin bude kular da ganin fuskarshi yayi ya dubi inda kamshi ke fitowa, la haula wala kuwati illa billah!!! Mikewa yayi ai ya saki baki wacece wannan yake gani haka Bilkisu ce kallonta kawai ya keyi bakinshi a bude da murufin kula a hannu tazo tayi dariya amma kuma sai ta kanne wata irin tafiya takeyi kamar batason taka kasa karayraya jikinta takeyi ta yanda ko ina nata motsi yakeyi, frige ta nufa ta wani dan duka ta zaro jug dinda ta saka drinks a ciki, a saman frige din ta jayo kofunan jug din guda biyu ta nufo dany din. Har yanzu tsaye yake yana kallonta kamar wata baindiya yake ganinaka shi ga baki daya yama rasa me yake ciki, yama manta da yunwarda yakeji shin wai Bilkisu ce haka, ajiye jug wani zaburar das hi. Cikin kissa da kisisina irinta wayayyin mata, sannan ta anshi murufin kular ta ajiye ta ciro flet ta zuba masu abinci ta ciro fork daya ta ajiye a gabanshi, gab aki daya rasa ta cewa yayi, to muna zaice daukar fook din yayi a sannan ne ya tuna da yunwarda yakeji ya fara cin abincin yana kai loma ta farko a baki lakuwati! Wani irin dadi yaji ya kamashi. Har kunne, ya kara dibo ta biyu ya ci sai a sannane ya lura Bilkisu bata ci, lafiya baka cin abincin ne ya tambaya yana kallonta bata fuska tayi kamar zatayi kuka dazu ne da ina fere doya na yanke hannuna Magana takeyi cikin salo irin na shagwaba, ajiye spoon din yayi mu gani sannu — injin bakiji ciwoba sosai, bari na dauko first aid box da kyar ta kanne dariyar da tayi kokarin fito mata yanda taga yanayi abin gwanin ban dariya dan taliki dukya rude, a’a ka basrshi kawai ya daina yimin zafi sosai, to bari na baki abinci ko da sauri ya fada yana dubanta, dama haka takeso nufinta kenan, daga kai tayi cikin shagwaba tace to, ci yakeyi yana har said a su duka suka koshi, sanna ta tashi ta zagayo ta zuba drinks din a kofi ta tattako dai-dai inda yake said a ta wani kwanta mishi sanna ta fara bashi a baki, rasa duniyar da yake yayi da mai zaiji dadin drinks din ko kuwa Balkisu da take kokarin zautarda shi,


nan take ya shanye, ta tambayeshi cikin wani irin kasha murya a karo tana wani murmushi mayen kallo daga kai kawai yayi batareda ya samu Kalmar eh ta fito ba, ta kara tsiya yamishi ta bashi a baki nanma ya shaye a karamaka ta sake tambaya sake daga kai yayi kamar wani dan karamin yaro wanda bai iya Magana ba, duk iya kannewanda tayi wannan karon said a tayi dariya ta yanda ba zai gane dashi take ba duk da tasan ya koshi baya dai iya cewa ya koshi ne said a ta fara tsiyayowa kafinta kai masa a baki, sai ji tayi ayi wani irin gyashi da kyar ta iya hadiye dariya tace anya Dearest baka kishi ba, na’am eh nakoshi gaskiya kam, saura ke mana kasha, daga kai tayi tareda fadin uhum ta tashi ta nufi kujerar ta a fara shan drinks din, kallonta yakeyi kamar bai taba, ganinta ba ita kuwa tana sha tana kallonshi yanda taga yanayi kamar zai hadiye ta saura kiris tag ware, tagama sai tace masa miasa na koshi, dan gajeren murmushi yayi tau, bata jira yace wani abuba ta fara daukan kaya tana kai kitchen, dama ai kin barsu sai gobe naga dare yayi kome kike gani, dare fah kace yanzu ko karfe tara tayi ne duba agogonshi yayi au da gaskiyarki fa tara da minti takwas ni ca nike dare yayi sosai goben na kai sauran wayanda bankai ba, shima murmushin yayi ba tareda yace komai ba, zo muje yau za’ayi wani film dinda nakeso sosai farin wata ta wuce kawai batareda ta jirashiba, da sauri ya taso ya biyota wane fil ne? Marokon zamani kasan ko sau nawa zan kalleshi bana gajiya taje ta kuma kayan kallo koda suka kawo harma an fara ta nemi go ta zauna shima ya zo kusa ta ita ya zauna, ta lura dashi, kamar yana so yayi wata Magana kawai yi tayi kamar bata ganeba, sai can yayi dan guntun tsaki, kinga nama manta banyi wanka ba, ni da nace ina zuwa ko abinci baznci ba zanyi Wanaka, dauko idanuwan ta tayi akan kallon da takeyi hakane fa kaga nima sam na manta, mikewa yayi yanufi dakii harda dan tuntubeshi, ya fada tailet yayi wanka sanna yasa wata doguwar riga baka ya dawo falo ya zauna wai yanzu naji wani irin iska yana shigowa juyowa tayi ay hark agama wankan, ita dai tasan baifi minti hudu da yabar falon ba wannan wane irin wankane haka ta danyi murmushi, eh harna kare mana ko kinga nayi sauri ne? a’a tambaya kawai nayi, wurin wani dariya akayi musa mai sana’a ne kun sanshi wajen iya acting dariya ta saka harda shakewa kallonta kawai yakeyi shi kwata-kwata baiga abin dariya acikinba sai a lokacin ya kula a yanda aka canza wasu abubuwa da yanda ta mayadda sauran lamination dinsu a falo, akice yau an canza tsarin gida oh! Wai sai yanzu kai ka gani dama ta fada tana dan noke kai gaskiya yayi kyau, murmushi kawai tayi, Bilkisu yau kinsha aiki, kika gyara gida haka sanna kuma kika dafa abinci da idan mutum yaci baya iya Magana akan dadi gaskiya im the luky husband in the whole universal kuma wai kinga yanda kikayi kyau kamar irin ‘yar tsawar nan Barbier kinyi kyau fiye da yanda kike tsmmani fah. Wani tashi tayi yanda tayi yana kodata haka, tashi yayi ya nufi inda take kashin kanta ya taba sannan kuma haka sai kace na indiyawannan dariya ta saka don Allah malam dadin bakin ya isa haka, Allah ba dadin baki nakeyi ba ni dai yau nama rasa me zanlawa tantaki dashi wurin haduwa murmushin dadi tayi tace “hauni” Balkisu kinsha aiki da yawa ya kamata ace kinje kin kwanta dariya ta yi tace waya gayama ba yaje ya kasha kayan kallo yace muje ka? Mikewa tayi tsaye amma sai duk ta wani langwabawa kamar zata fadi yadai yafada, kafafuwana ne sukeyimi nauyi cikin shagwaba, ai cak ya dauketa ya shiga daki.


Balkisu ke faman gudu wani katon mutum yana binta kuwwa take ta faman bugawa amma ba kowa a wajen a jikin wani bango ta fada, shi kuwa katonan ya tsaya a gabanta ya rutseta kuwwa kawai take famanyi, hannu daya yasa ya shaketa a hannu dayan shi kuwawata irin wukace doguwa daga wukar yayi sama dana kokarin soka mata wukar yayi sama girgiza kai takeyi tana fadin a’a duk idanuwanta sun firfito alamun firgita, amma koa jikin katon nan, da karfi ya nasa mata wukar ta kwala uwar kara mai tsnanin karfi. Maigado!!! Da karfi ummah ta farka tana kururuwar kiran sunan diyarta firgigi shima malam iro ya fara a sakamakon hargowar da yaji matarshi tayi. Lafiya? Meke damuwanki? Me akayi? A firgice tace mai gado? Maigado! Wani ne da wuka ——– ta kasa idarda zancen duk ta firgita da ummunan mafarkinda tayi dakata ba sai kin fadi abinda kikayi mafarki ba sherin shedan ne kawai shi yakeso yayi wasa da tunaninki, tukunna ma dai kinyi addu’a ne kafin ki kwanta sai da tayi shiru na dan lokaci har a lokacin a firgice take sannan ta tuna da batayi addu’a ba a sakamakon dan kishin gidawa kawai tayi bacci ya shareta a’a banyi ba ta amsa masa kingani ko shedan ne kawai shi yasa addu’a takeda muhimmanci a rayuwar musulmi tayama za’ayi mususlmi ya kwanta baiyi addu’a ba wadda idan kayita ba aljani ba har mutum bai isa ya cutar maka ba, wallahi dan kishingidawa nayi bansan sa’adda ma bacci ya kwasheni ba malam, amma ina ganin kamar Bilkisu tana cikin wani mummunan haline ko kuma wani mummunan abu yana shirin faruwa da ita ni naji —– don Allah kibar wayannan shirmen baxaki nemi wuri ki kwanta kawai daga kinyi mafarki, to ance miki mafarki gaskiyane, shifa mafarki kasha biyu ne, na alhairi daga Allah ne na sharri kuwa daga shedan Bilkisu na can lafiya kalau da mijinta ba ke kika gayamin da rana cewa ta kiraki kunri wata hart ace tana gaidani, ba? Daga kai kawai tayi alamar ah kiyi addu’a kawai ki kwanta Bilkisu na lafiya kalau ba kuma ba abinda zai same ta sai alkhari da iznin Allah. To malam, harta fara addu’a sai kuma ta juyo ta dubashi tace malam kanada kudi a waya na kirata naji hankalina zaifi kwanciya? Kira! Zanzu kinsan ko karfe nawa ki kira ta yanzu cikin wanna tsohon daren abin ma ai gwanin ba dariya, yarinya da mijin ta haka kawai ki kirasu yanzu ki tada masu da hankali ko, ba halin ta kara cewa wani abu domin ta lura maigidan nata ya fara hasala dole tayi addu’a ta kwanta ba domin tana jin wani bacci ba sai domin hakan ya zama dole gareta ne, sam bacci kasa daukar ta yayi ita kawai tasan abinda ta gani Allah dai ya nuna mata goobe da safe lafiya dole ta kira taji ya ake ciki. A bangaren malam iro kuwa tabbas yasan maid akin sa taji tsoro sosai dangane da mafarkinda tayi amma ba yadda zai yi dole wannan hanyar dayabi ita kadai zai yi domin ya tasa abin a zuciyanta karshe yazo ya dameta, Hmm koma da menene Allah ya fefaddashi ya juyoshi zuwa alkhairi amen haka dai yayi ta sake-sake ba tareda ya dade ba bacci yayi awon gaba dashi. Tunda sassafe ummata aika aka siyo mata kati ta bayar aka saka mata a waya number Bilkisu ta danna ta kira. Ita kuwa Bilkisu tana diney suna break fast da dearest dinta sai ringing din wayarta taji, tashi tayi ta nufi saman kujera inda wayar ke faman kara o wake kirana da sasssafen nan, dubawanda zatayi taga Ummarta ce da sauri ta dauka salam alaikum umma ina kwana, lafiya ba wata matsala umma, muna cikin koshin lafiya, Umma lafiya dai ko dariy atayi sanna tace to ummah, amen,amen, amen umma mungode, zaiji ahan sai anjima ina gaida abba sosai ummah, tau amen umma nagode, to sai anjima aha, ta katse wayar ta ajiyo ko lafiya umma keta faman jeromata tambayoyi haka, wanna addu’a tasha bamaban da irin addu’oin da umma keyi masu a kullum, sauri tayi ta kore wanna tunani ta koma dany, wayene? Sulaiman ya tambaya, umm ace tace tana gaida kai Allah sarki ina ansawa lafiya take dai ko lafiya kalau take bilkisu ta amsa, ya mutan gidan ina fatan kowa lafiya ko? Kowa lafiya kalau madallah, please in kunji waya ina gaidasu koda yake idan ma naje office inada niyar na kirasu, mikewa yayi ya shiga daki ya dauko mukullin mashin dinshi ya fito bari na wuce to karna makara har kofar gida bilkisu ta rakashi, koda yake tai iyyar ta bude gate din cewa kawai yayi ta rike mashi, bayan ya fitada mashin din kuma ya dawo ya rufe da kanshi wai shin baya son ta wahala ita dai dariya kawai takeyi tad an rakashi waje, ai kinfita yayi can I have a pot? Ya tambaya yana yar kasha murya dariya tayi tace no langabewa yayi kamar mai shirin kuka please don Allah, fashewa tayi da dariya yadda taga yayi said a tasa hannu daya ta rufemai idanu sannan ta yimasa kiss a kumatu, wani dogon ajiya zuciya yayi thanks a lot matata kin biya yanzu zanje office da karfi suka fasa dariya su duka ya fito da nufin hawa mashin dinshi ita kuwa tana bayanshi wani tsoho sukeyi kicibis dashi zaune a kusa da gidan su kanshi na duke ga dukan alamu yana neman taimako. Nauyin mutanen da yaji yasa ya daga kanshi su Bilkisu ya gani suna kallonshi cike da tausayi yauwan yaro don Allah ko da akwai abinda zaku taimakamin dashi wallahi ina neman taimako, hannu Sulaiman yasa a aljihu ya zaro dari biyar ya bashi ga wannan da hanzari ya karba nawa zan shire dauka nab aka baba, dauka! Nagode, nagode Allah ya saka da alkhairi Allaah ya biyaka amen kawai Sulaiman yace yah au mashin, har ya tada mashin din Bilkisu tace mashi bari na kawo mishi sauran break fast dinmu, yauwa jeki kawo masa ya tada mashin ya wuce, ita kuwa Bilkisu ta shiga gida ta zuba masa ragowar abincin da sukaci ta fito waje ta kawo masa, nagode, nadoge Allah ya biyaki, Allah yak are ku daga sherin duk wani mai sharri, gaskiya kunada hankali da nutsuwa kun dace sosai, kinyi dacen miji, shin kuwa yayi dacen mata, allah ya barku tare ya baku zuri’a dayyiba, murmushi tayi tace amen, har a ranta taji dadin kalaman shon nan ta shige gida ta rufe kofa. Wai Bilkisu yau har wanka nawa zakiyi ne Sulaiman ya tambayi Bilkisu wadda take ta faman goge jiki da tawel, dariya tayi, ko wanka nawa nayi dai-dai nike ai, domin yanada kyau ga kowace matar aure ta kansance mai yawan wanka tana tsafface jikinta, domin (bad ordour) is natural wanan ga duk wani wanda shekarunsa suka kai, ba ko  a son duk wata macen aure mijinta ya shaki wannan smell din, (adressing mirrow) ta zauna bayan kamala jawabinta, hakane your bighness sulaiman yace tareda mikewa akan gado ya bude, bandaki ya shiga, guntun murmushi tayi ta zaro (comp) ta fara shace kanta, zara comp din ta sakeyi a gashinta me zata gani!! Ga baki dayan inda ta shace duka gashinta ya cire saura ya fadi kasa sura kuwa yana a jikin comp din, kamar dai wadda ta saka (cliffer) ta aske wurin haka wurin yayi, wurgi tayi da (comp) din ta mike tsaye ta fara ja da baya tana kallon taswirar ta a cikin dressing mirrow din, ga baki daya gashin saman kanta zubewa yakeyi yana yankewa daga lokacin duka gashin ya zube cikin kankanin lokaci, ba suma ko daya kamar wadda tayi aski da rega. Wata irin karat a buga mai tsanani karfi, a guje Sulaiman ya fito daga cikin bandaki, ga baki daya ta fita hayyacinta, gam yariketa Bilkisu lafiya! Bilkisu! Sumana! Sumana! Kawai take kira, me ya faru da sumanki nuna masa mudubin tayi dad an yatsa,


me sumanki tayi kai hannu yayi ya taba sumanta, dai-dai lokacinda ta kai dubanta ya zuwa madubi, me zata gani kuma!! Sumanta dai yananan kalau ba abinda ya sameshi, cak ta tsaya kamar abinda aka zarewa lakka, baya-baya ta ringa ti shi kuwa Sulaiman yana riketa tama rasa ta inda zata fara, wasu zafafan hawaye suka rika zubowa takan kumatunta, kuka takeyi baji bagani gabaki daya al’amarin gidanan ya isheta wannan wace irin rayuwace mai dauke da firgici da tashin hankali, a hakikanin gaskiya dab a domin tana yiwa Sullaiman HUBBIL YAKIN bad a ba abinda zai hana ta gudu ta koma garinsu ko zata tsira daga wannan ukuba, Sulaiman ya shiga aikin sa rarrashin ta ya ringa yi tareda yimata nasifa akan komai yayi tsanani saukin na nan zuwa, a haka suka kwana kowa da abinda yake sakawa a nashi ran ka shegari Bilkisu tayi kokarin ta sharar da abinda ya faru da dare bayan sunyi break fast tar aka mijinta kamar kullum, fitarsu keda wuya suka yi kicibis da tsohonnan da suka saba taimakawa a kwanakin baya. Gaidashi sukayi da yar fara’ar su, da hanzari ya amsa shima yana mai nuna fara’arshi a fili kamar wanda ya dade da sanin su, wannan karon ma Sulaiman dari biyar ya bashi yah au mashin dinshi yayi gaba, ita kuwa Bilkisu taje ta zuba mashi ragowar abinci, yayi sallama yawuce sannu a hankali suka fara sabawa das hi, har y azan idan ya dade bai zo ba, daga bisani ya zo sukan tambayi dalili. Sun shaku matuka da juna har sunayimasa kallo a matsayin dan uwan shima kuwa yana yi masu kallon diya. Bilkisu ce zaune a falo taci wanka harta gaji tana kallo, sallama taji ana rangada wa, da hanzari taje ta bude kofa su Fatima ne suka kawo mata ziyara taje ta bude kofa sannunku da zuwa ku iso. Makotan ta ne su Khadija da Fatima suka kawo mata ziyara. Sannun ku fad a zuwa ku zauna, taje ta kawwo musu abinsha ta ajiye musu, ta nemi gu itama ta zauna, bayan sun dan karba abinda ta kawo musu Fatiman ta fara da cewa Amarya bakya laifi ko kin kasha yar masu gida murmushi kawai tayi rufamin asiri ta fada wanna kwalliya haka ai sai ki hana angon ki fita waje, wannan karon dariya tayi ni dai don Allah kurufamin asiri. I fira suka ringayi da juna abin gwanin ban dariya, gaskiya su Fatima akwaisu da raha abinda ya dauke hankalinsu daga firar da sukeyi wani film dinda akayi na india mai suna Ghajini film din yayi kyau sosai. Sun dan dade suna fira kafin Khadija ta daga kai ta kai dubanta ya zuwa wani karon inlargement na Bilkisu da mijinta Sulaiman a lokacin aurensu, Wow!! Masha allah! Ta fada batareda tasan a baiyane ta fada ba tsananin kam da sukayi yadda suka yi kama da juna baka sai kace ‘yan biyu, agaskiya sunada kama sosai da mijinta kuma ba kananan indiyawa bane wajen kyau, su duka sun yaba da kyan ilargement din tare da fatan ganin yadda ya yansu zasu kasance ta fannin kyau. Ita dai Bilkisu bata samu ta cewa ba kyalesu tayi sukayi ta zuba abinsu sai da suka tashi zasu wuce Bilkisu ta rakasu kamar wadda ta tunada wani abu da hanzari ta tambayesu, ina ake kitso nan unguwar don Allah? Me kike nufi? badai tunda kikazo maigidan keyi miki kitso ba Fatima ta fada suka bushed a dariya ga baki dayansu. A’a wata yar office dinsu yake kaini gidanta takemin to bata iya irin wanda nake so ba wibin kawai ta iya kullum abin daya mukeyi abin duk ya fara isata. Anan bayan mu kuwa akwai wata inna Kande ko wane irin kitso kike so ta iya, amma da wuya ki gane gidan daga kwatance idan dai kika tashi kibiyo ta gidanmu ma hadaki da Habiba yar aikin mu sai ta kai ki. To ni ko gobe ma ba sai tazo ta kaini koda yake ba sai kinzo ba ma aikota goben ta kaiki. Kin san halinmu da surutu kar kizo mu tsaidaki.


Dariya tayi tace ina jira har garka tar aka su sukayi bankwana suka wuce ita kuwa ta dawo daga cikin tana dariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

error: Alert: Content is protected !!